1al' adun malam bahaushe.2adabi. 3kirar jimla?


To get notifications when anyone posts a new answer to this question

Answers (1)

Post your comment

Smashing
6 years ago

Al'ummar Hausa dai, al'umma ce dake
zaune a arewa maso yammacin tarayyar
Nijeriya da kudu maso yammacin
jamhuriyyar Nijar. Al'umma ce mai dimbin
yawa, sun bazu a cikin kasashen Afirka da
kasashen Larabawa kuma a al'adance
masu matukar hazaka, akalla akwai sama
da mutane miliyan hamsin wadanda
harshen Hausa shi ne asalin yarensu. A
tarihi kabilar Hausawa na tattare a
salasalar birane. Hausawa dai sun sami
kafa daularsu ne tun daga shekarun
1300's, sa'adda suka sami nasarori da
dauloli kamar su daular Mali, Songhai,
Borno da kuma Fulani.
A farko-farkon shekaru na 1900's, a
sa'adda kabilar Hausa ke yunkurin kawar
da mulkin Aringizo na Fulani, sai Turawan
Mulkin Mallaka na Birtaniya suka mamaye
arewancin Nijeriya, da kuma kafa
manufofin mulkin bayan gida, a bisa
karkashen mulkin Birtaniya,'yan mulkin
mallaka sai suka marawa Fulani baya na
cigaba da manufofin Aringizon siyasarsu,
har yanzu dai mulkin gamin gambiza
tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi
kane-kane a arewacin Nijeriya.
Kodayake, Hausawa na farko-farko
maharba ne, amma da zuwan Addinin
Musulunci da kuma karbarsa da hannu
bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam.
Ginshikokin al'adun Hausawa na da
mutukar jarunta, kwarewa da sanayya
fiye da sauran al'ummar dake kewayenta.
Daura Kasace wacce a kasani mai dadewa
da tarihi a kasar Hausawa.
Sana'ar noma ita ce babbar sana'ar
Hausawa, sabo da ingancin noma;
Hausawa ke wa sana'ar noma kirari da
cewa, "na duke tsohon ciniki kowa ya zo
duniya kai ya tarar", akwai kuma wasu
sana'o'in kamar su sha'anin jima watau
harkar fatu, rini, sa'a da kira, fannonin
dake mutukar samun cigaba a harkokin
sana'o'in Hausawa. Hausawa dai sun jima
da shahara wajen harkar fatauci kana
kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin
yau da kullum, tare da masu mulki da
masana.
Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma
mafi sanayyar harshe a nahiyar Afirka,
harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga
wasu harsuna musamman Larabci kana
kuma harshen na tafiya tare da yanayin
mu na zamani bisa al'adar cudeni-in
cudeka. Harshen Hausa dai ya zama
harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a
da ba Hausawa bane a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, akwai cincirindon al'ummar
Hausawa a manyan biranen yammacin
Afirka da arewacin Afirka da kuma
yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa
da kuma yankunan da Hausawa suka jima
suna bi a hanyar ta zuwa aikin Hajji.
Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi
da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a
rubutun ajami da aka buga tun kafin
zuwan Turawa 'yan mulkin mallaka na
Birtaniya. Har ila yau, kuma wani tsarin
rubutu a ajami da aka kirkiro tun kafin
zuwan Turawa, da ba kasafai ake amfani
da shi ba yanzu.

Quick Questions